Iran Da Qatar Sun Tattauna Game Da Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliya Da Kuma Alaka Tsakanin Kasashen Biyu.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, kan ci gaban da ake samu a dangantakar kasashen biyu da kuma farfado da yarjejeniyar nukiliya.
A yayin ganawar ta wayar tarho, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a bangarori daban-daban na siyasa, tattalin arziki da kuma ofishin jakadancin.
Kuma bisa la’akari da tattaunawar da jami’an kasashen biyu suka yi a baya wajen tuntubar juna da musayar ra’ayi da takwaransa na kasar Qatar dangane da muhimmin taron gasar cin kofin duniya na FIFA da aka gudanar a kasar Qatar da kuma fannonin hadin gwiwa a wannan fanni.
A cikin wannan tattaunawa ta wayar tarho, Amir Abdollahian ya kuma yi ishara da shawarwarin dage takunkumin, ya kuma jaddada aniyar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na cimma yarjejeniya mai kyau, mai karfi da dorewa.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Qatar ya yi nuni da muhimmancin tuntubar juna kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai bayyana shirin kasarsa na yin hadin gwiwa da Iran a fagen wasannin gasar cin kofin duniya ta FIFA da ake yi a Qatar.
Ya yi ishara da matsayar Iran masu ma’ana, yana mai bayyana ci gaba da tattaunawa don soke takunkumin da cewa yana da muhimmanci.