Iran Da Qatar Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyoyin Raya Tattalin Arzikin Kasashen Biyu.
Kwamitin tattalin arziki da kasuwanci na kasashen Iran ta Qatar sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama yau litinin a birnin Doha na kasar Qatar, wanda ake ganin zai kara bunkasa yawan musayan kayaki da khidimomi tsakanin kasashen biyu.
Majiyar muryar JMI ta bayyana cewa, ministan makamashi na kasar Iran Ali-Akbar Mehrabiyan ne ya jagoranci tawagar kasar Iran a taron kwamitin tattalin arziki na kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi wadanda suka hada da bangarorin, Transit wato yada zango, tafiye-tafiye, da jigilar kayaki, masana’antu, kasuwanci, kwaston, da yankunan budaddun kasuwanni, lantarki, yawon shakawata, al’adu noma da kuma wasannin.
READ MORE : Iran Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Taimaka Wa Al’ummar Falastinu.
A shekarar da ta gabata dai kasashen biyu, wato Iran da Qatar sun yi musayar harkokin kasuwanci wanda ya kai dalar Amurka miliyon 150, amma a wannan karon suna son kara fadada shi zuwa bangarori masu yawa.
READ MORE : Isra’ila Ta Sake Kaiwa Siriya Harin Makamai Masu Linzami.
READ MORE : Iran Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wata Mujami’a A Najeriya.
READ MORE : Barazanar ruwa; Wani mummunan mafarki wanda ya sanya juriya ga Tel Aviv.