Iran da Qatar Sun Rattaba Hannu Kan Wasu Yarjeniyoyi Na Hadin Gwiwa Guda 6.
Iran da gwamnatin Qatar sun rattaba hannu kan wasu takardu da yarjejeniyoyin guda shida domin bunkasa hadin gwiwa a fannin sufurin jiragen sama a lokacin gasar cin kofin duniya.
Rahoton ya ce, Iran da gwamnatin Qatar suka rattaba hannu a kan wasu takardu da yarjejeniyoyin 6 domin bunkasa hadin gwiwa a fannin sufurin jiragen sama, da kuma wasu ayyuka a lokacin gasar cin kofin duniya.
Wannan yarjejeniya ta hadin gwiwa tsakanin Iran da Qatar a fannin zirga-zirgar jiragen sama za ta kunshi bangaren aikin sufurin jiragen ruwa, da kuma wasu tanade-tanaden hadin gwiwa don tallafawa gasar cin kofin duniya ta Qatar.
Tun kafin wannan lokacin dai Iran ta sanar da cewa za ta bayar da dukkanin hadin kai ga kasar ta Qatar domin taimaka mata a bangarori daban-daban, domin samun nasarar daukar bakuncin gasar.
READ MORE : Ci gaba da aikata laifukan yahudawan sahyoniya tare da shahadar Bafalasdine.
A nata bangaren Qatar wadda take da kyakkyawar alaka da Iran, ta bayyana matakin da cewa ci gaba ne na ayyukan da kasashen biyu suke yi domin cin moriyar juna, tare da yabawa da kuma godewa mahukuntan kasar ta Iran kan hadin kan da suke bata.