Iran Da Oman Sun Tattauna A Kan Wasu Batutuwa Da Suka Shafi Gabas Ta Tsakiya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian da takwaransa na kasar Omani Badr bin Hamad al-Busaidi sun yi shawarwari ta wayar tarho kan batutuwan da suka shafi ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da ma na kasa da kasa.
Baya ga haka kuma sun tattauna batun shawarwarin da ake yi tsakanin Iran da manyan kasashen duniya domin farfado da yarjejeniyar shirin nukiliya na Iran.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya ce, abin da yake da muhimmanci shi ne kowane bangare ya sauke nauyin da ya rataya a kansa, wajen yin abin da ya dace, kuma dukkanin tsaiko da ake samu kan batun yana fitowa ne daga bangaren Amurka.
READ MORE : Sakon Tel Aviv zuwa Yamma; Idan ba ku fuskanci Hizbullah ba, samar da iskar gas ba shi da matsala.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Oman ya tabbatar da cewa, kasarsa taa nan kan bakanta na ganin cewa ta bayar da dukkanin gudunmawar da za ta iya, domin cimma sakamako na karshe a wadannan shawarwarin, da kuma tabbatar da cewa an dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata.