Iran Da Mali Zasu Karfafa Alakar Dake A Tsakaninsu A Fagage Da Dama.
Kasashen Iran da kuma Mali, sun kudiri anniyar karfafa alakar dake a tsakaninsu a fagage da dama.
Bangarorin sun cimma wannan matsaya ce yayin ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Mali, Abdoulaye Diop, ya kai Tehran.
Yayin ziyarar tasa Mista Diop, ya gana da takwaransa na Iran, Hossein Amir-Abdollahian, inda Iran ta ce a shirye ta ke ta yi musaya da Mali a fanoni da dama da suka shafi kimiya, masana’antu kiwon lafiya da dai sauransu.
Kasashen kuma sun tattauna kan batutuwan da suka shafi yankin da kasa da kasa dama batutuwan da suka shafi alakar dake a tsakaninsu.
A nasa bangare Ministan harkokin wajen kasar ta Mali, ya ce kasarsa na fatan karfafa alaka da Iran ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci, sannan kuma ya gayyaci takwaran nasa na Iran, da ya ziyarci kasar ta Mali cikin gajeren lokaci.