Iran Da Mali, Sun Yunkuri Aniyyar Karfafa Alakar Dake A Tsakaninsu.
Kasashen Iran da Mali, sun bayyana anniyarsu ta karfafa alaka a tsakaninsu ta fagage da dama.
Wannan bayyanin na kunshe a taron manema labarai da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka gudanar a daura da ziyarar da ministan harkokin wajen Iran ke yi a kasar Mali.
Da sanyin safiyar yau Talata ne ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Hossein Amir Abdolahian ya isa kasar Mali, a ran gadin da ya fara a wasu kasashen Africa.
Mista Abdolahian ya gana da takwaransa na Malin, Abdolaye Diop, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen biyu da ma na kasa da kasa.
Abdolahian dai na tare da rakiyar tawagar ‘yan kasuwa da masu zuba jari na kasar ta Iran.
Yayin ziyarar Iran ta baiwa Mali wani bangare na alluran riga kafin cutar korona miliyan daya samfarin Barekat ta Iran da ta yi alkawarin baiwa kasar cen baya.
READ MORE : Kasashen Turai Na Fama Da Fari Mafi Muni A Shekaru 500 Da Suka Gabata.
Nan gabe ne kuma ake san ministan harkokin wajen aksar ta Iran zai isa kasashen Tanzania da Zanzibar a ci gaba da ran gadin nasa a nahiyar ta Africa.