Iran Da Kuwait Sun Tattaunawa Kan Batutuwa Da Suka Shafi Gabas Ta Tsakiya.
Iran ta cea shirye take ta hada karfi da Kuwait domin kara fadada shawarwari a tsakanin kasashen yankin gabas ta tsakiya.
Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir Abdollahian ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Kuwait Ahmad Nasser Al-Sabah.
A yayin wata tattaunawar wadda ta gudana ta wayar tarho a yammacin jiya Juma’a, Amir Abdollahian ya bayyana aniyar Tehran na karfafa dangantakarta da Kuwait da kuma raya tattaunawar yankin, yana mai bayanin cewa: Gwamnatin Iran tana jaddada muhimmancin da hadin gwiwa mai amfani a tsakanin kasashen yankin.
Ya ce a cikin tsarin siyasar Iran da ta fi baiwa fifiko har da tabbatar da kyakkyawar alaka da makwabtanta, bisa la’akari da cewa, irin wannan hadin gwiwa yana daga cikin abubuwan da za su sanya kasashen su ci moriyar juna, musamman ta fuskar ayyukan tsaro, da kuma ci gaban yankin a dukkanin harkokin na tattalin arziki da cinikayya da bunkasar ilimi.
Amir Abdollahian ya yi ishara da matakin tsagaita wuta na wucin gadi a kasar Yemen, inda ya bayyana cewa Iran tana maraba da hakan, tare da jaddada bukatar kawo karshen kai hare-hare da kuma aikewa da kayan agaji ga al’ummar kasar ta Yemen cikin gaggawa.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya kuma yi tsokaci kan sabbin abubuwan da suka faru a tattaunawar Vienna da nufin janye wa Iran din takunkumin.