Iran Da Gaske Take Tana Bukatar Yarjeniya Mai Karfi Dangane Da Dage Mata Takunkuman Tattalin Arziki.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Husain Amir Adullahiyan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran da gaske take kan cewa tana bukatar cimma yarjeniya mai karfi tsakaninta na Amurka dangane da dage mata takunkuman zaluncin da ta dora mata, amma hakan ba duk yadda ta zo ba.
Tashar talabijin ta Presstv anan Tehran ta nakalto Abdullahiyan yana fadar haka ne a shafinsa na Instegram a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa ya zanta tokwarorinsa na kasashen UAE.Qatar, Omman da kuma Iraki kan wannan batun ta wayar tarho, inda ya shaida masu cewa Amurka ce bata nuna cewa tana son a dagewa Iran wadannan takunkuman ba.
Amma kasar Iran ta gabatar da hanyoyi daban-daban don bawa Amurka zabi kan hanyoyoyin da yakamata a bi don warware matsalar takunkuman tattalin arzikin kan kasar Iran, amma babu wata matsaya na kirki da ta dauka.
READ MORE : Shugaban Kasar Faransa Ya Ce Rasha Tana Amfani Da Abinci A Matsayin Makami.
Har’ila yau ministan yayi maganar cewa gwamnatin kasar Iran mai ci ta sanya karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen makobta a matsayin babban al-amari a wajenta. Don Iran Iran zata kara gaggauta batun karfafa dangantaka da kasashe makobtanta.