Iran; Cibiyar Sararin Samaniya Ta Karbi Sakonni Na Farko Daga Tauraron Dan’adam Mai Suna “Khayyam”.
Ma’aikatar sadarwa ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa cibiyar sararin samaniya ta kasar ta karbi sakonni na farko daga tauraron dan’adam mai suna Khayyam wanda aka cillaci a jiya Talata, sa’o’ii kadan bayan ya hau kan falaki mai tazarar kilomiya 500 daga doron kasa.
Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP ya tauraron wanda aka gina a cikin gida zai yi ayyuka da dama daga ciki, zai taimaka wajen tabbatar da tsaron kan iyakokin kasar Iran, ayyukan noma, albarkatun karkashin kasa da kuma hasashen bala’o’in dabi’a.
Labarin ya kara cewa a yau Talata ce aka cilla tauraron dan’adam mai suna Khayyam kirar kasar Iran a cibiyar cilla taurarin dan’adam na kasar Rasha da ke kasar Kazakistan. Kuma shi ne aiki hadin guiwa na farko tsakanin kasar Iran da Rasha dangane da ayyukan sararin samaniya.
READ MORE : Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 10 a luguden wuta kan Zirin Gaza.
READ MORE : Kashe mutum 10 da Isra’ila ta yi a Gaza ya harzuƙa Falasɗinawa.