Iran; Batun Falastinu Shi Ne Mafi Muhimmanci Ga Duniyar Musulmi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi Allah-wadai da sabbin hare-haren wuce gona da iri da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan masu ibada a harabar masallacin Al-Aqsa da ke tsohon birnin Quds, yana mai cewa batun Palastinu shi ne babban abin da al’ummar musulmi suka sanya a gaba.
“Muna ganin cewa al’amarin farko na al’ummar musulmi wato Palastinu, ya shiga cikin wani hali na kara rincabewa, Gwamnatin yahudawan sahyoniya suna da yaudara suna kokarin ganin bayan lamarin,” Saeed Khatibzadeh ya fadi hakan a wani taron manema labarai na mako-mako a birnin Tehran.
Ya kara da cewa har yanzu Falasdinu ita ce batu mafi muhimmanci na al’ummar musulmi, ba tare da la’akari da makircin da gwamnatin Tel Aviv ke kullawa a kan hakan ba.
Khatibzadeh ya kuma bayyana cewa, batun Falasdinu shi ne babban lamari mafi fifiko ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kuma dukkanin kasashe masu son ‘yanci da ke adawa da wariya.
Jami’in diflomasiyyar na Iran ya ce; daidaita huldar diflomasiyya tsakanin wasu kasashen Larabawa da Isra’ila ya karfafawa Isra’ila gwiwa wajen ci gaba da aiwatar da ayyukan ta’addanci.
READ MORE : Rikici a Saudiyya da Kuwait game da dokar hana Doctor Strange 2.