Shugaban hukumar koli ta kare hakkin bil’adama na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata kyale ‘yan ta’adda su sami sakat a ko ina suke ba a duniya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kazem Gharibabadi, babban sakataren hukumar koli ta kare hakkin bil’adama ta kasar Iran yana fadar haka a jiya Laraba a wani taro na tattauna batun gurfanar da Amurka a gaban kotunan kasa da kasa kan take hakkin mutanen kasar Iran.
Gharibabadi ya bayyana cewa ya zuwa yanzu kungiyoyin ‘yan ta’adda wadanda suke samun goyon bayan Amurka da kuma wasu kasashen yamma sun yi sanadiyyar mutuwar Iraniyawa 17,000.
Don haka yace Jamhuriyar musuluncin ba zata taba bawa yan ta’adda daman saki da walwala ba, a ko ina suke a duniya.
A wani bangare na jawaninsa Garibabadi ya ce a halin yanzu gwamnatin kasar Amurka a karan kanta ta dorawa kashe kimani 30 takunkuman tattalin arziki wadanda basa bisa ka’ada ta kasa da kasa, kuma Iran ce a gaba a cikin jerin wadannan kasashe.
Daga karshen babban sakataren hukumar koli ta kare hakkin bil’adama na kasar Iran ya ce ba zai manta da yadda Amurka ta hana iraniyawa samun magunguna yaki da cutar Korona a dai dai lokacinda kasar take fama da cutar a cikin kasar ba, wanda hakan ya jawo rasa rayukan mutane da dama a kasar.
Ya ce idan da gaske ne Amurka ta damu da mutanen Iran kamar yadda take riyawa ta daukewa kasar takunkuman tattalin arziki na zalunci da ta dorawa kasar.
Kasar dai ta iya jurewa matsain lambar takunkuman tattalin arzikin kasashen turai wanda ya tilastawa kasashen na turai neman a zauna a teburin tattaunawa domin sulhu domin ganin cewa takurawa mafi tsananin da amurka da kawayen ta suka yima kasar lokacin Shugaba Trump baiyi tasiri ba.
Source: ABNAHAUSA