Iran An Yi Wa Jagora Allurar Riga Kafin Korona Ta Uku.
A Iran, an yi wa jagoran juyin juya halin musulinci na kasar allurar rigakafin cutar korona ta uku samfarin «COV-Iran Barekat» da kasar ta samar.
Jim kadan bayan karbar allurar Jagoran, ya bukaci dukkan ‘yan kasar dasu yi koyi da hakan, wadanda kuma basuyi riga kafin ba su gaggauta yin hakan.
A cewar jagoran, ‘’kin yin allurar riga kafi da kuma kin sanya takunkumi, take hakkin wasu ne, wanda kuma barazane ne ga kiwon lafiyar al’umma’’
A ranar 23 ga watan Yulin bara ne, akayi wa jagoran juyin juyin juya halin na Iran allurar ta korona karo na biyu.
Alkalumman da hokumomin kiwon lafiya a Iran suka fitar sun nuna cewa Kawo yanzu mutum miliyan 61 ne da dubu 112 da 617 suka karbi allurar korona ta farko, sai kuma miliyan 54 da dubu 505 da 698 da sukayi allurar ta biyu, yayin da mutum miliyan 19 da 646 da 357 suka karbi allurar ta uku.
Jimmilar allurar riga kafin da akayi a fadin kasar ya tasa sama da miliyan 135.