Wani dan bindiga kuma ma’aikacin wani kamfanin tsaro ya bindige Ayatullahi Abbas-Ali Soleimani, a kusa da wani banki a garin Babolsar na lardin mazandaran a arewacin kasar Iran a safiyar yau Laraba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran IRINN, a tashar talabijin sa na labaransa waace ta nakalto gwamnan lardin Mazandaran Seyyed Mahmoud Hosseinipour yana cewa Ayatullahi Soleimani ya rasu jim kadan bayan an kai shi asibiti sannan an kama wanda ya kashe shi, an kuma fara bincike don gano dalilan da suka kai ga kashe babban malamin.
Kafin rasuwarsa dai Ayatullahi Soleimani mamba ne a majalisar kwararru masu zaben jagoran juyi juya halin musulunci, sannan ya taba rike mukamin wakilin jagora a laradin sistan Buluchistan na kudu maso ganacin kasar.
Majalisar kwararru masu zaben jagora dai ita ce majalisar mafi girma a kasar Iran saboda, majalisar mujtahidai ne wadanda suke da aikin kula da ayyukan jagoran juyin juya halin musulunci, sannan tana da damar tube shi ko kuma zaben wadanda zai maye gurbinsa bayan rayuwa ko kuma tubewa.