Iran; Amurka Na Kokarin Haifar Da Rikici A Yankin Yammacin Asiya.
Iran, ta ce Amurka na kokarin haifar da rikici a yankin yammacin Asiya ta hanyar amfani da manufofinta na kyamar Iran, inji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran.
Nasser Kan’ani na mai da martani ne ga sabbin kalaman shugaban Amurka Joe Biden, wanda ya zargi Iran da tayar da tashin hankali a yankin na yammacin Asiya, a jawabin da ya yi a taron kasashen Larabawa na yankin a birnin Jeddah na kasar Saudiyya ranar Asabar.
Mista Kan’ani ya bayyana kalaman na shugaban Amurka a matsayin marasa tushe wadanda kuma ba za a amince da su ba, yana mai cewa, “Irin wadannan zarge-zarge marasa tushe sun yi daidai da manufofin Washington na tada fitina da haifar da tashin hankali a yankin.”
Ya kara da cewa Amurka ita ce kasa daya tilo da ta yi amfani da makaman kare dangi sannan kuma a baya-bayan nan, sannan ga tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen yankin.
READ MORE : Kuwait; Cibiyoyi 28 Sun Fitar Da Bayani Na Nuna Aadawa Da Duk Wani Mataki Na Kulla Alaka Da Isra’ila.
Ya ce, manufar Iran ita ce amfani da fasahar nukiliya ta zaman lafiya bisa tsarin dokokin kasa da kasa.