Iran; Amurka Da Turai Ba Su Da Wani Zabi Da Ya Wuce Su Amince Da Yarjejeniyar Nukiliya.
Mataimakin shugaban kasar Iran kan harkokin tattalin arziki, Mohsen Rezaei, ya bayyana cewa, Amurka da Turai ba su da wani zabi da ya wuce amincewa da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto Rezaei yana cewa, “Manufar harkokin wajen gwamnatin Raisi na amfani da dukkan karfin da take da shi wajen huldar kasashen waje, tana daukar manufa madaidaiciya, da kuma yin mu’amala da dukkan kasashen dake cikin tsarin manufofin gwamnati da muradun gwamnati,” in ji Rezaei.
Ya kuma yi ishara da cewa Iran ta samu nasara a cikin manufofin harkokin waje a cikin ‘yan watannin nan.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta kammala nazarin sharhin da Iran ta yi kan kudirin Tarayyar Turai na komawa kan yarjejeniyar nukiliya.
READ MORE : Iran Ta Ce A Shirye Take Ta Yi Hulda Da Kasashen Africa Wajen Hakar Man Fetur Da Iskar Gas.
Washington ta ce ta mika wa Brussels martaninta dangane da mahangar Iran game da “sigar karshe” ta yarjejeniya.
READ MORE : Mayakan Falasdinawa sun kai hari kan motar jami’an tsaron yahudawan sahyoniya.
READ MORE : Kotun Saudi Ta Yankewa Tsohon Limamin Ka’aba Daurin Shekara 10 a gidan yari.