Iran; Amurka Ba Zata Dorawa Kasar Ra’yinta Tare Da Zarge-Zarge, Ko Takunkumi Ba.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya bayyana cewa idan akwai sauran hanyar diblomasiyya da ta rage a tattaunawar dagewa Iran takunkuman tattalin arziki to al-barkashin kasar ne, amma gwamnatin Amurka mai ci bata bar wata kafar dimlomzasiyya dangane da yarjejeniyar JCPOA ba sai da ta toshe shi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abdullahiyan yana fadar haka ne a shafinsa na twitter a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa gwamnatin shugaban Biden na Amurka tana kan abinda ta gana daga gwamnatin Trump na takurawa Iran har sai ta dawo kan bukatunta, wanda ya tabbata cewa wannan bai zai yi amfani a kan kasar Iran ba.
READ MORE : Japanawa Na Ban Kwana Da Tsohon Firaministan Kasar Shinzo Abe.
Ministan yana maida martani ne ga waji jawabin da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya fada, wanda kuma jaridar Washington post ta buga, kan cewa ya ci gaba da dorawa Iran takunkuman Trumo sannan a watan da ya gabata ma ya kara sanyawa wasu daddaikun mutane a iran takunkuman tattalin arziki har sai kasar ta dawo kan yarjejeniyar JCPOA.
READ MORE : Shugabannin Kasashen Rasha, Turkiyya Da Iran, Zasuyi Taro Kan Siriya A Tehran.
READ MORE : Biden ba zai iya magance kiyayyar da aka yi wa gwamnatin sahyoniya da tafiya guda ba.