Iran; Abdullahiyan Ya Bayyana Damuwarsa Ga Lafiyar Jami’an Diblomasiyyar Kasarsa A Afganistan.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hosain Amir Abdullahiyan ya bayyana irin damuwar da gwamnatin kasar Iran take ciki dangane da lafiyar jami’an diblomasiyyarta a kasar Afganistan.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka ne a jiya Asabar a lokacinda yake zantawa da tokwaransa na kasar Afganistan ta wayar tarho.
Abdullahiyan ya fadawa Amir Khan Muttaqi ministan harkokin wajen kasar Afganistan kan cewa gwamnatin Iran tana bukatar cikekken tsaro ga jami’an diblomasiyyarta a ofishin jakadancinta da ke birnin Kabul, da kananan ofisoshin jakadancinta da suke Kandaharm Mazar-Asharif da kuma Jalalabad.
A nashi bangaren Amir Khan Muttaqi ya bayyanawa Abdullahioyan rahoton dangane da harkokin tsaro a kasar ta Afganistan, ya kuma kara da cewa makiya kasashen biyu bas a son ganin dangantaka mai karfi tsakanin kasashen biyu musulmi kuma makobta.
READ MORE : Hamas; Za’a Fara Babbar Yaki Da Isra’ila Bayan Ramadan.
Daga karshe ya tabbatarwa Abdullahiyan kan cewa jami’an tsaron kasar Afgansitan a shirye suke su kare dukkan jami’an diblomasiyyar kasar Iran da suke Kabul da kuma wadanda suke aiki a kananan ofisoshin jakadancin kasar a wajen Kabul.
READ MORE : Ma’aikata A Najeriya Sun Gudanar Da Bukin Ranar Ma’aikata Ta Duniya.