Iran A shirye Take Ta Tallafawa Kasar Qatar Wajen Karbar Bakunci Gasar Cin Kofin Duniya.
Babban direktan hukumar kula da tashoshin jirgin ruwa na kasar Iran ya fadi cewa Iran za ta tallafawa kasar Qatar wajen karbar bakunci gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya da hukumar fifa za ta shirya a wanan shekarar ta 2022, a matsayinsa na babban taro da za’a yi a yankin, kuma damace ga iran na samar da kudaden shiga a cewarsa.
Za’a gudanar da gasar cin kofin duniya karo na 22 ne a kasar Qatar daga ranar 21 ga watan nuwamba zuwa 18 ga watan Decembar shekara ta 2022 kuma na farko a irinsa da za’a yi a yammacin yankin asiya.
Wannan yana zuwa wane a daidai lokacin sarkin Qatar sheikh Hamad bin Tamin Al-thani ya zanta da shugaban kasar iran IbrahimRa’isi ta wayar tarho, inda shugaban iran ya taya shi murnar shiga watan Ramadan kana ya nuna gamsuwarsa game da shirin Qatar na karbar bakuncin gasar cin kofin duniya,
READ MORE : WHO; Mafi Yawancin Alummar Duniya Na Shakar Gurbatacciyar Iska.
Har ila yau ya bayyana shirin Iran na bada dukkan taimakon da ake bukata a tsaibirin Kish da yammacin kasar Iran wajen gudanar da wasu wasannin na cin kofin duniya ta hanyar da ta fi dacewa .