Iran ta ce za ta tattauna da manyan kasashen duniya da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyarta a farkon watan Nuwamba.
Khatibzadeh ya ce, gwamnatin Shugaba Ebrahim Raisi da ke da kasa da kwanaki 55 da darewa karagar mulki, ba ta tunanin shirya tattauanawar za ta dauke ta sama da kwanaki 90, yana mai cewa, Iran za ta shirya ganawar a tsakiyar watan Nuwamba mai zuwa.
Wannan shi ne karon farko da Iran ta sanya lokaci don yiwuwar komawa kan teburin tattaunawa.
Yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 ta dan saukaka wa Iran takunkumai saboda matsin lamba kan shirinta na nukiliya, wanda Majalisar Dinkin Duniya ke sa ido.
Shugaban Amurka na wancan lokacin Donald Trump ya janye kasar daga yarjejeniyar da ta kunshi bangarori daban-daban, sannan ya fara saka wa kasar takunkumi a shekarar 2018, abin da ya sa ta sake dawo da shirinta na nukiliyar sannu a hankali tun daga shekarar 2019.
A wani labari na daban wanda kuma ya ja hankalin mutanen duniya sakamakon fitar da wasu mahimman takardu da ke bayyana yadda dimbim fitattun mutane a duniya suka boye tarin dukiyoyi da suka kai miliyoyin Dala a asusun ajiyar kasashen ketare da babu haraji, gwamnatoci sun yunkuro don rage tasirin wannan tonon sililin na binciken da aka yi wa lakabi da ‘Pandora Papers’.
Sunayen wasu shugabannin 35, tsaffi da masu ci ne suka bayyana a wasu kundaye da suka kai akalla miliyan 11 da dubu 900 da aka bankado daga cibiyoyin kudi a fadin duniya wanda aka yi wa lakabi da ‘Pandora Papers’.
Cikin wadanda sunayensu suka bayyana a wandannan kundaye ,akwai tsohon Fiiraministan Birtaniya, wanda aka nuna ya kauce wa biyan harajin kan wani gidansa na birnin Landan.
Babu sunan shugaban Rasha Vladimir Putin, amma kuma an danganta shi da wasu kadarori na makusantansa a birnin Monaco na Faransa, musamman wani gida na kusa da teku, mallakin wata mata da suka haihu da ita.
Sai dai kakakin fadar Kremlin ta Rasha, Dmitry Peskov ya ce, zargi ne mara tushi.
Ita ma Jordan ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin watsi da rahoton cewa ,an bankado tarin kadarori da suka kai miliyan 100 na Dala da Sarki Abdallah na biyu ya tara a California da Landan.
Cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa ta gudanar da wannan bincike, wanda kafofin yada labarai da suka hada da Washington Post, BBC da Guardian suka watsa.