Iran A Shirye Muke Mu Ci Gaba Da Tattaunawa Da Saudiya Cikin Mutunci.
Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasar Saudiya har zuwa lokacinda zasu kai ga fahintar juna.
Tashar talabijin ta “Khabar” a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake zantawa da wayar tarho da firai ministan kasar Iraki Mustafa Al-Kazimi a jiya Asabar.
Sayyid Ibrahim Ra’isi ya kuma godewa kasar Iraki a shiga tsakani da take yi tsakanin kasashen biyu. Sannan ya bukaci gwamnatin kasar Iraki ta yi abinda zata iya yi don ganin an dakatar da yaki a kasar Yemen.
Daga karshen shugaba Raisi ya kammala da cewa kasar Iraki tana da matsayi na musamman a wajen Jumhuriyar Musulunci ta kasar Iran. Don haka a cikin shirinta na kwautata dangantaka da kasashe makobta, kasar Iraki tana da matsayi na musamman wajen hulda da ita.
A nashi bangaren firai ministan kasar Iraki Mustafa Al-Kazimi ya bayyana cewa kasarsa tana son ganin an kara dankon zumunci a tsakananin kasashen biyu a dukkan bangarori.