Rundunar sojin Iraki ta ce ta kakkabo wasu kuramun jirage biyu dake shawagi a kan sansanin sojin Amurka dake kasar, wata guda bayan an yi yunkurin kai hari sansanin da wani jirgin soja mara matuki.
Wannan wani sabon dabarun kai farmaki da mayaka dake samun goyon bayan Iran ke amfani da shi, na dada tada hankalin hukumomin Amurka da Iraki.
Lamarin da yasa Amurka ta sanya wata na’ura domin kakkabo jirage marasa matuki a saman sansaninta na Ain al-Asad, da yake yammacin saharar Iraki, wanda ya yi nasarar dakile wannan hari, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana.
Babu dai wata kungiya da ta dauki nauyin wannan hari na ranar Lahadi.
Amurka dai ta ta shiga kasar iraki ne ba bisa son ran mafi yawancin mutanen iraki ba kuma tun wancan lokaci ake ta samun tashe tashen hankula a kasar wanda ya sabbaba asarar rayuka da damangaske.
Kasar Iran itace makociya kuma ‘yar uwar kasar Irakin kuma a kwai takun saka mai girma tsakanin ta da amurkan wanda hakan ya sa amurkan ta dage sosai wajen tabbatar da wanzuwar ta a kasar duk da manya manyan matsalolin da take fuskanta.
An samu kungiyar ‘yan kasa masu sa kai karkashin fatawar babban malamin kasar Ayatullah Sistani da kuma sahhalewar gwamnatin kasar in da suke yaki da mamayar amurka.
Kasancewar kungiyar al’umma ta Hashd Al-sha’abi a kasar ya kawo sauki sosai da sosan gaske a bangaren tsaro da bangarori da dama na siyasa zamantakewa da dai sauran su.
A baya bayan nan ne dai amurka ta kashe kwamandan rundunar sojin Iran tare da sauran abokan aikin sa da suka hada da Abu mahdi Almuhandis wanda ba’irake ne kuma shugaban rundunar sa kai ta Hashd Al-Sha’abi.
Ana cewa amurka bata taba shiga kasa ta fita duk da asarar dukiya da sojoji da take tafkawa baya ga kashe fararen hula da sojojin na amurka suka shahara dashi.