Ya ce halin yanzu rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta riga ta gama kammala tsare-tsarenta a bangaren ayyukan tsaro a lokacin wadannan taruka, inda jami’an dubu 20 ne aka ware domin wannan aiki.
Ministan harkokin cikin gidan na Iraki ya ce, ya zama wajibi su dauki irin wadannan kwararan matakan na tsaro, bisa la’akari da matsalolin da aka rika samu a lokutan baya na hare-haren ‘yan ta’adda lokacin tarukan addini a kasar.
Yanzu haka dai jama’a daga sassa daban-daban na kasar Iraki sun fara yin tattaki zuwa birnin Karbala domin halartar tarukan na arba’in da za su gudana a ranar 20 ga wannan wata na Safar da muke ciki.
A wani labarin na daban shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, dakin karatu na birnin Iskandariyya a kasar Masar na ajiye da takardun tafsirin kur’ani mafi jimawa a duniya, wanda ake kira da tafsirin Albusti, wanda Abu Ishaq Bin Ibrahim Albusti ya rubuta shi, wanda ya rasu shekara ta 307 bayan hijirar manzon Allah daga Makka zuwa Madina.
Tun daga wancan lokaci wannan tafsiri ake kula da shi shekaru bayan shekaru, wanda daga karshe dai ya isa dakin karatu na birnin Iskandariyya, wada yake dauke da littafai masu tarin yawa da aka rubuta su shekaru masu yawa da suka gabata a cikin takardu da fatunsu na asali.
Baya ga tafsirin ayoyin kur’ani, akwai hadisan ma’aiki a cikin littafin, wadanda suke bayani kan ayoyi da kuma bayanin saukarsu.
Sannan kuma an rubuta a cikin shafuka 233, kuma a cikin shafi akwai shedara 21 da tsarin rubutu da ake kira magribi.
Nadiya Al-sharif ita ce shugabar bangaren baje koli na babban dakin karatu na birnin Iskandariya, ta bayyana cewa akwai dadaddun littafai makanatan wannan da yawansu ya kai 120 a cikin wannan dakin karatu da ake adana su.