Kasashen Masar da Jordan da Iraki sun amince da batun daukaka hadin kai ta fannin tsaro da tattalin arziki a tsakaninsu, yayin wata ziyara da shugaban Masar ya kai Iraki a karon farko cikin shekaru 30.
Wannan ziyarar da shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi da sarkin Abdallah na 2 na Jordan suka kai birnin Bagadaza na zuwa ne a daidai lokacin da Iraki ke kokarin matsowa kusa da kasashen Larabawa.
Zalika Iraki na neman karfafa kanta a matsayin mai shiga tsakani a tsakanin kasashen Larabawa da Iran, bayan da aka ruwaito cewa ta karbi bakoncin tattaunawa tsakanin Iran da Saudiyya.
Sisi da Abdallah sun gana da shugaba Barham Saleh da Firaminista Mustafa al-Kadhemi, inda ma Saleh yake cewa haduwar tasu wani sako ne mai karfi ga duniya, a cikin yanayin da yankinsu ke fama da kalubale.
Taron tsakanin Kadhemi da bakin nasa ya tattauna batutuwa da suka shafi yankinsu, gami da laluben hanyoyin yaukaka hadin kai tsakanin Iraki, Jordan da Masar a fannin tsaro, makamashi da kasuwanci, da kuma babbar matsalar falasdinu wacce ke karkashin zaluncin haramtacciyar kasar isra’ila, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa a bayan taron.
Sun kuma tattauna batun bijiro da masalaha a rikicin Syria da ya shekara 10, daidai da manufofin musulmi kuma larabawa.
Wannan yunkuri dai shine irin sa na farko amma ana ganin kamar yunkuri ne na fatar baki, domin dai ana so a gani a kasa.
Kasashen lababawa na yankin gabas ta tsakiya musamman yankin falasdinu na fama da babbar matsalar barazanar haramtacciyar kasar isra’ila amma sauran kasashen larabawa sun zura idanu san ta kashe raunanan falasdinawa babu ji babu gani.
Idan da gaske kasashen Iraki, masar da jordan da gaske suke ana sa ran a samu babban canji a nahiyar ta gabas ta tsakiya kuma hakan zai sanya a samu fahimtar juna tsakanin kasashen larabawan da jamhuriyar musulunci ta Iran wacce ke daya daga cikin kasashen na larabawa a gabas ta tsakiya.