Sakataren Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Ƙasa (IPMAN), James Tor, ya bayyana rikicin Isra’ila da Iran a matsayin babban dalilin ƙarancin man fetur da ake fama da shi a Najeriya.
A cikin ‘yan kwanakin nan dai ƙarancin man fetur ya haifar da dogayen layuka a gidajen mai baya ga tsada da kuma tashin farashin sufuri.
Da yake tsokaci kan ci gaban da aka samu a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na ARISE, James ya bayyana irin rawar da Gwamnatin Tarayya ke takawa wajen shigo da albarkatun man fetur da kuma ware su ga masu ruwa da tsaki ciki har da Ƙungiyar IPMAN domin rabawa.
Ya yi nuni da cewa, tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin Gabas ta Tsakiya a halin yanzu, sun ƙara taɓarɓarewar ƙalubalen da ake fuskanta, wanda ya haifar da cikas a harkar samar da kayayyaki.
Sai dai ya ce Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya ƙara himma wajen ganin an shawo kan lamarin ta hanyar buɗe gidajen man fetur domin tabbatar da wadatuwarsa a faɗin ƙasar.
Ya ce, “Mutanen da ke shigo da man fetur a ƙasar nan Gwamnatin tarayya ce.
“Kuma idan sun shigo da waɗannan kayayyaki, sai su ba mu, mu masu ruwa da tsaki a harkar domin rabawa.
“Saboda haka abin da muke samu ne za mu iya bayarwa. Idan babu, to ba za mu iya ba da wani abu ba.
“Amma Gwamnatin Tarayya tana iya bakin ƙoƙarinta. Domin ko a ranar Litinin ɗin nan, Shugaban Ƙasa ya yi bayanin cewa NNPC zai buɗe wasu matatun man fetur domin mu samu isasshen man fetur da za a raba wa jama’a.
Matsalar ƙarancin man fetur a Najeriya na ƙara tsanani musamman a manyan biranen kasar a daidai lokacin da ƙungiyar dillalan man da kamfanin NNPC ke ci gaba da fitar da bayanai da ke sabawa juna a kan matsalar.
An dai ɗauki matakin nuna wa juna yatsa a kan wannan matsala ta ƙarancin man fetur ɗin da ke ƙara ƙamari a kusan ɗaukacin birane da ƙauyukan Najeriya, inda matsalar ta jefa jama’a cikin mawuyacin halin.
IPMAN ta bayyana cewa kodayake akwai ƙarancin man amma ɗimbin bashin da suke bi na Naira biliyan 200 ya ƙara ta’azzarar lamarin a cewar Alhaji Sirajo Kamba Yahya Kamba, shugaban masu wuraren adana mai na ƙungiyar ta Najeriya.
NNPC ya dage cewa akwai wadataccen mai domin ’yar matsala ce kawai aka samu kuma an shawo kanta.
DUBA NAN: Harin Iran Kan Isra’ila Ya Bude Sabon Shafi
Najeriyar dai duk da wadatar man fetur da take da shi har yanzu ta kasa magance matsalar ƙarancin man da ake fuskanta daga lokaci zuwa lokaci duk da janye tallafin da ta yi, da kuma ikirarin miƙa mafi rinjayen kaso na harkar hannun ’yan kasuwa.
Daga Aliyu Jalal Da Jamilu Adamu