Rundunar ‘yan sanda ta kasa da kasa Interpol ta samu nasarar kame mutane akalla dubu 1 da 400, tare da kwace dala miliyan 7 da dubu 900 yayin jerin sumamen da ta kaddamar a sassan nahiyoyin Turai da Asiya.
Cikin sanarwar da ta fitar, Interpol ta ce a yayin da akasarin jama’a ke kallon gasar Kwallon kafa ta turai a matsayin magoya baya, daruruwan jami’ai na musamman a tsakanin kasashe 28 sun shirya samun haramtattun miliyoyin kudade daga caca tare da hadin gwiwa da kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka da suka kware wajen almundahanar kudade.
Kawo yanzu, sumamen da Interpol ta yi wa take da SOGA wanda kuma ta kaddamar har sau takwas ya ba ta nasarar kame mutane sama da dubu 19,000, kwace kudade fiye da dala miliyan 63, da kuma rufe haramtattun gidajen caca dubu 4000 a sassan Turai da Asiya.
A wani labarin na daban jami’an ‘yan sandan China da na Afrika ta Kudu sun kwace dubban rigakafin coronavirus na bogi kamar yadda Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasa ta sanar.
Kazalika jami’an tsaron sun kuma gano takunkumai na bogi, sannan kuma suka kama wasu Sinawa da mutanen Zambia da aka samu cikin harkar.
A can kasar China kuwa, rundunar ‘yan sandan ta yi nasarar gano wani gungun miyagu mai sayar da alluran rogakafin Covid-19 na bogi a wani bincike da ta kaddamar wanda Hukumar Interpol ta dauki nauyi.
A samamen da ‘Yan sandan suka kai a Chinar, sun cafke mutane 80 tare da kwace rigakafin na bogi fiye da dubu 3 da aka sarrafa a wata haramtacciyar farfajiya.
Tun a farkon wannan shekarar ce, Hukumar ‘Yan sandan Kasa da Kasa ta gargadi hukumomin kasashen duniya cewa, su daura damarar tunkarar wani gungun miyagu da ke shirin samar da haramtaccen rigakafin coronavirus a zahiri da kuma yanar gizo.