Ingila; Ranar Litini Za’ayi Jana’izar Elizabeth II.
Fadar Buckingham a Ingila ta tsayar da ranar gobe Litinin 19 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a yi wa Sarauniya Elizabeth ta biyu jana’izar kasa.
Sanarwar da fadar ta fitar ta ci gaba da cewa za a yi jana’izar ne a Westminster Abbey da ke birnin Landan.
Yau ne dai za a dauko gawar Sarauniyar daga fadar Balmoral inda ta rasu ranar Alhamis, inda za a yi tafiyar sa’a shida da gawar cikin tsanaki zuwa Edinburgh.
Za a bai wa jama’ar kasar damar ban kwana ga Sarauniyar a yayin da za a ajiye gawarta a fadarta ta Edinburgh, kafin a wuce da ita zuwa birnin Landan.
Kafin nan dai a jiya Asabar ne aka nada Sarki Charles na uku a matsayin sabon Sarkin na Ingila, a wani biki da ya gudana a Fadar St James da ke birnin London.
Majalisar nada sarki ce ta tabbatar da Charles na uku a matsayin sabon Sarkin.
READ MORE : Kasashen Turai Na E3, Sun Fara Bin Isra’ila Game Da Yarjejeniyar Nukiliya.
Babban dan Sarauniya Elizabeth II, mai rasuwa, ya zama Sarki ne kai tsaye ranar Alhamis, amma a bisa tsarin sarautar sai majalisar ta tabbatar da matsayinsa.