Dubban mutane ne suka yi dandazo yau alhamis a tsakiyar birnin London don gudanar da shagulgulan taya Sarauniya Elizabeth murnar cika shekaru 70 akan karagar mulkin Ingila, a wani gagarimin shagali da ake ganin ya iya zama na karshe a tsawon lokacin da ta dauka ta na mulki.
Tuni aka fara mabanbantan faretin ban girma ga Sarauniyar ingila mai shekaru 96 wadda ake sa ran za fito bainar jama’a har sau biyu yayin shagulgulan a gab da fadar Buckingham.
Tun da sanyin safiya, daruruwan jama’a daga sassan Birtaniya da kuma wasu daga wajen kasar suka rika dafifi tare da tattaruwa a gab da fadar ta Buchingham galibinsu dauke da furannin girmamawa.
A watannin baya-bayan nan ne aka fara jita-jitar yiwuwar gudanar da kasaitaccen biking a Sarauniya Elizabeth duk da yadda Basarakiyar ta takaita shiga cikin jama’a tun a bara saboda wahalar da yawan zama da tashi ke bata da kuma tsoron cutar Covid-19.
Sarauniya Elizabeth ita ce mafi dadewa akan karagar mulkin Ingila bayan gado daga hannun mahaifinta sarki George na 6.
A wani labarin nmai kama da wannan yau Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta cika shekaru 98 a duniya, inda rundunar sojin Birtaniya ta gudanar da bikin karrama ta, ta hanyar fareti da kuma harba bindigogi kamar yadda aka saba gudanarwa.
Sashen makadan sojin da ake kira ‘Coldstream Guards‘ sanye da jajayen kaya da huluna na kawa, sun buga taken karrama Sarauniyar a fadar ta dake Windsor a Yammacin Birnin London. Rahotanni sun ce an ci gaba da harba bindigogi a sassa daban daban na kasar Birtaniya ciki harda tsaunin Landan da akafi sani da Turanci a matsayin ‘London Tower’.
Sai dai Sarauniyar, wadda itace shugabar kasa mafi yawan shekaru a duniya, ta gudanar da bikin cika shekaru 96 ba tare da wasu hidimomin da aka saba ba, inda ta koma yankin Sandringham domin gajeruwar hutu.
Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da aike mata da sakon taya murna.