Mataimakin shugaban cibiyar hasashen yanayi ta kasar Sin Zhang Hengde, ya bayyana cewa, yanayi a kasar Sin ya samu kyautatuwa a shekarar 2022.
Jami’in ya bayyana cewa, a shekarar 2022, matsakaicin alkaluman PM 2.5, alkaluman da ake amfani da shi wajen auna gurbacewar iska, ya ragu da kashi 3.3 bisa 100 a shekara a kasar Sin.
Zhang wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai, ya bayyana cewa, matsakaicin adadin kwanakin da aka yi fama da yanayi na hazo a fadin kasar a bara, ya kai kwanaki 19.1, raguwar kwanaki 2.2 idan aka kwatanta da shekarar 2021.
Zhang ya kara da cewa, daga watan Mayu zuwa Oktoba na shekarar 2022, kididdigar da aka auna yanayin na gurbatar yanayi na laimar ozone, ta karu da kashi 9.7 bisa 100 bisa makamancin wannan lokacin a shekarar 2021, saboda raguwar kwanakin da aka yi ruwan sama da kuma yanayin matukar zafi . (Ibrahim)
A wani labarin na daban ofishin kula da harkokin zirga-zirgar kumbuna dake dauke da ‘yan sama jannati na kasar Sin ya ba da labarin cewa, ‘yan sama jannati na kumbon Shenzhou-15 sun kammala ayyukansu cikin nasara, sun kuma dawo birnin Beijing a yau da safe.
Bayan da suka iso birnin Beijing, za a kebe ‘yan sama jannatin uku don a binciki lafiyarsu da ba su lokacin hutu, ta yadda za su samu farfadowa. Daga baya, za su zanta da ‘yan jarida a birnin.
A ranar 29 ga watan Nuwamban shekarar 2022 ne, aka harba kumbon Shenzhou-15 daga cibiyar harbar tauraron dan Adam ta Jiuquan, daga bisani ne kuma ya hade da tashar Tianhe a sararin samaniya.
‘Yan sama jannatin 3 sun gudanar da ayyukan nazarin kimiyya da dama, tare da yin tattaki a waje sau 4, matakin da ya aza tubali ga manyan ayyukan kimiyya da fasaha da za a yi a nan gaba. (Amina Xu)