Indiya za ta sayi man fetur daga Rasha a farashi mai rahusa.
Indiya na duba yiwuwar sayen man fetur da wasu albarkatu daga Rasha a farashi mai rahuwa, inji wani rahoton kamfanin dillancin labarai Reuters.
Rahoton na cewa wasu jami’ai biyu ne suka sanar da Reuters wannan aniyar ta Indiya.
Kasar Indiya na sayen kashi 80 cikin 100 na dukkan albarkatun man fetur daga kasashen waje ne, kuma a ciki tana sayen kimanin kashi 2 zuwa kashi 3 cikin 100 na albarkatun man daga Rasha.
Tana bukatar man na Rasha ne saboda farashin mai na tashin goron zabi a kasuwannin duniya, gwanatin Indiya na bukatar rage yawan kudin da ta ke kashewa kan makamashi.
READ MORE : Shin me nene laifukan yaki kuma ko za a iya tuhumar Putin kan Ukraine?
Wani jami’in gwamnatin Indiya ya ce kasar na farin cikin sayen man na Rasha kuma ba ta damu da barazanar takunkumi da kasashen yammacin duniya ke yi wa dukkan wadanda suka yi hulda da Rasha ba.
Jmai’an na Indiya sun kuma ce aiki yayi nisa kan samar da wani tsari na sauya takardun kudin kasashen biyu wato daga Rupee zuwa Rouble.
READ MORE : Rasha Da Ukraine Zasu Sake Tattauanwa Yau Litini.