A hukumance Indiya ta mika ragamar shugabancin G20 ga Brazil a bikin rufe taron shekara-shekara na kungiyar, wanda aka gudanar a New Delhi a karshen makon nan.
Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya mika mulki ta hanyar mika wa shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula, da Silva takardar shedar zama shugaban kasa.
Indiya ta kasance shugaban kungiyar G20 tun ranar 1 ga watan Disamba, lokacin da ta karbi ragamar mulki daga Indonesia, za ta ci gaba da rike mukamin har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba.
A yayin taron na kwanaki biyu, kungiyar ta amince da sanarwar bai daya, wadda ta dauki alkawura kan batutuwa da dama, da suka hada da samar da abinci da makamashi, da sauyin yanayi, da kuma rangwamen bashi a duniya.
Modi, a ranar Lahadin da ta gabata, ya kuma ba da shawarar tantance matsayin shawarwari da mambobin suka gabatar da kuma tantance “yadda za a iya hanzarta gabatar da su”.
“A wannan zaman, za mu iya yin nazari kan batutuwan da aka yanke a yayin wannan taron,” in ji Modi, ya kara da cewa za a raba cikakken rahoto ga mambobin.
Source: LEADERSHIPHAUSA