Indiya Ta Harba Wa Pakistan Makami Mai Linzami Bisa Kuskure.
Ma’aikatar tsaron Indiya ta sanar da yin nadamar harba wani makamai mai linzami bisa kuskure da rundinar sojin kasar yi kan kasar Pakistan.
Ba’a dai samu hasarar rai ba a harbin wanda Indiya ta ce ta yi nadama akansa.
Sanarwar ta ce a cikin gyara da ake lokaci zuwa lokaci an samu ‘yar matsala wacce ta kai ga harba makamin a ranar Laraba wanda kuma ya fada a wani yankin Pakistan.
Saidai ma’aikatar tsaron ta Indiya, ba ta yi bayyani ba kan nau’in makamin da ya kubuce mata a fada a Pakistan, saidai ta ce an kaddamar da bincike a matakin koli kan lamarin.
Sanarwar ta Indiya ta zo ne, ‘yan sa’o’I bayan da ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta fiatar da sanarwar yin tir da keta hazonta ta hanyar wani abu mai gundun tsiya.
Ta kuma kira jakadan Indiya a Islamabad, domin bayyana masa takaicin kasar game da lamarin da ta ce ya lalata gidaje sannan ya jefa rayuwar fararen hula da kuma jiragen sama a sararin samaniyar kasar cikin hadari.
READ MORE : Tsohon Shugaban Kasar Zambia Rupiah Banda Ya Rasu.