Wasu fusatattun mazauna kauyen Raghunathpur dake kasar Indiya sun kama wata narkekiyar kada tare da kokarin fasa cikinta domin ceto rai.
Wasu jama’a dake kusa da kogin Chambal sun tabbatar da cewa sun ga lokacin da kadar ta hadiya Antar Singh, yaro mai shekaru 7 yayin da yake wanka Jama’ar sun fito da kadar daga kogin tare da bude bakinta gudun ta tauna yaron, amma jami’ai sun kwaceta saboda sun ce babu tabbacin ita ta hadiye kadar.
Wasu fusatattun mazauna kauyen Raghunathpur, yankin Madhya Pradesh Sheopur dake Indiya sun cafke kada domin yanka cikinta su fito da yaro ‘dan shekaru bakwai da ta hadiye da ran shi.
Kadar ta kai wa yaron mai suna Antar Singh farmaki lokacin da yake wanka a kogin Chambal a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli kuma ta ja shi har cikin kogin.
Jama’ar yankin da suka ga lamarin da ya faru sun yi kira ga iyalai da ‘yan uwan yaron da suka yi gaggawar zuwa kuma suka kama kadar da taimakon sanduna, igiya da kuma raga. Sun ja ta wajen kogin.
Babban jami’in dan sanda da jami’in kula da dazuka sun isa yankin tare da hana su kashe katuwar kadar. Sun gamsar dasu kan cewa sun nemi yaron a Chambai.
“Don haka, sun kamata kuma suka daure ta tare da saka katako a tsakanin hakoranta domin tabbatar da cewa bata tauna yaron ba,” wani mazaunin yankin yace.
Cike da tashin hankali ‘yan uwan yaron ke kiran sunansa ‘Antar Singh’ tare da fatan cewa yana nan da rai yayin da ake jan kadar daga cikin ruwa.
Sun cigaba da tirsasa jami’an kula da daji kan cewa a fasa cikin kadar domin fito da yaron amma suka ki bada kadar. Daruruwan mutane sun taru a wurin.
A daya bangaren, rundunar SDRF ta cigaba da neman yaron a kogin Chambal. Tawagar ceton ta kai yammaci amma bata ga ko alamar yaron ba.
An dakata da nemansa bayan da duhu yayi. Jami’ai sun sanar sa mazauna kauyen cewa, idan kadar ta kama yaron, ba za ta hadiye shi ba.
‘Yan sanda sun ce ta yuwu yaron ya shiga wuri mai zurfi ne na kogin, za a cigaba da nemansa a ranar Talata.
Mazauna kauyen sun ce kadar ta na cin mutane kuma a dauketa tare da sakinta a wuri mai nisa. Kamar yadda jami’ai suka ce, akwai daruruwan kada a kogin kuma an dinga samun farmakinsu da suke kai wa mutane.
Sai dai, wasu daga cikin mazauna kauyen sun yi ikirarin cewa sun ga lokacin da kafar ta hadiye yaron da ransa.
Source:Legithausang