Fitacciyar mawakiyar Bollywood wadda wakokinta suka yi suna a fina-finan India Lata Mageshkar ta mutu a safiyar Lahadi 6 ga watan Fabrairun 2022.
Mawakiyar ta mutu tana da kimanin shekaru 92 a duniya bayan an kwantar da ita a asibiti sakamakon cutar korona.
Likitocin da suka yi mata magani a lokacin tana asibitin sun ce ta samu matsala ne da wasu daga cikin sassan jikinta kamar huhu.
- Bollywood: Fina-finai 4 da Salman Khan ya ƙi yi amma suka sa Shahrukh Khan ya shahara
- Sonia Mann: Tauraruwar India da ta yi watsi da fina-finan domin goyon bayan manoma masu zanga-zanga
- Bollywood: Abin da ya kashe auren Aamir Khan da matarsa Kiran Rao na shekara 15
An haifi mawakiyar ne a ranar 28 ga watan Satumbar 1929 a jihar Madhya Pradesh.
A tsawon rayuwarta dai ta rera wakoki fiye da dubu talatin a harsuna da dama kamar Hindi da Marathi, kuma tun tana kimanin shekara 5 a duniya ta fara waka koyon.
Lata Mageshkar, ta bayar da gudunmuwa da dama a bangaren fina-finan Bollywood saboda irin wakokin da ta yi wadanda ba za a taba manta da su ba.
Tuni Firaiministan India Narendra Modi, ya yi ta’aziyya a kan rasuwarta a shafinsa na tuwita, haka suma sauran jaruman Bollywood sun mika na su sakon ta’aziyyar a shafukansu na sada zumunta.
Gwamnatin India dai ta ayyana zaman makoki na kwana biyu wanda zai fara daga ranar Lahadi 6 ga watan Fabrairun 2022 zuwa 8 ga watan in da a lokacin zaman makokin za a yi kasa da tutar kasar a ko ina a fadin India.
Za a yi mata jana’izar ban girma ta kasa in da ake sa ran halartar manyan mutane kama daga jami’an gwamnati zuwa fitattun ‘yan Bollywood dama sauran al’ummar kasar.
Lata Mageshkar, ta samu lambobin yabo da dama saboda irin rawar da ta taka wajen rera wakokin da ake mata lakabi da mai muryar zinariya.
Tana da ‘yan uwa kamar Asha Bhosle, da sauran ‘yan uwan ta da mutu ta bari.
Daga cikin fitattun fina-finan da Lata ta yi wa wakoki sun hadar da, Aradhana, da Silsila da Dil To Pagal Hai da Shakti da Shree 420 da Aandhi da Azaad da Ek Thi Ladki da Amar Prem da Mohabbatein da Dilwale Dulhaniya Le Jayenge da dai sauransu.