Hukumar kula da makamashi ta duniya (IEA) ta bayyana fargabar cewar yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine na iya yiwa yaki da sauyin yanayi zagon kasa.
Shugaban na (IEA) Birol yace yana cikin damuwa dangane da barazanar da yaki da sauyin yanayin ke fuskanta saboda yakin dake gudana a Ukraine.
Hukumar a cikin wannan wata ta bayyana cewar an samu Karin kashi 6 na sinadarin dake gurbata muhalli a shekarar da ta gabata wanda ya kai sama da tan 36 a daidai lokacin da tattalin arzikin kasashen duniya ke farfadowa sakamakon annobar korona.
Suma kasashen Yammacin duniya na cike da damuwa dangane da samun makamashin tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.
A wani labarin na daban kuma Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki manyan kasashen duniya, inda ya ce sun aikata babban laifi saboda yadda suka yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu. Kalamansa na zuwa ne bayan fitar da wani sabon rahoto kan illolin sauyin yanayi, inda ya zargi manyan kasashen da ta’azzara matsalar.
Rahoton ya kuma bukaci tuhumar wadannan manyan kasashe na duniya saboda yadda suka gaza wajen daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar.
Mista Guterres ya bayyana cewa, kusan rabin al’ummar duniya na rayuwa cikin gagarumar barazana a yanzu, yayin da sukurkucewar alaka tsakanin halittu da muhalli ta kai matakin kololuwa a cewarsa.
Magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa, babu yadda za a karyata batun cewa, lallai hayaki mai gurbata muhalli shi ne ummul-haba-i-sin sauyin yanayin.
Sannan ya ce, watsi da nauyin da ya rataya akan shugabannni na matsayin babban laifi, kuma manyan kasashen duniyar da suka fi gurbata muhalliu, su ne da laifin cin amanar doran duniyar da muke rayuwa a ciki a cewarsa.
An dai fitar da rahoton kwararrun ne na Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da rikcin Rasha da Ukraine ke daukar hanklulan kasashen duniya.