Shugaban Kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) a Duniya Francesco Rocca ya cacaki kasashen Turai saboda abinda ya kira yadda suke nuna banbanci wajen kula da bakin da suka fito daga Ukraine da kuma wadanda suka fito daga nahiyar Afirka.
Shugaban na ICRC ya ce tabbas akwai nuna harshen damo tsakanin wadannan kasashe wajen yadda suke karbar bakin da suka fito daga wadannan bangarori biyu, ganin yadda suke rungumar wadanda suka fito daga Ukraine da kuma nuan kyama ga wadeanda suka fito daga Afirka.
Shugaban na ICRC yace banbanci tsakanin mutumin da ya tsere daga Donbas dake kasar Ukraine da kuma wanda ya gudu daga yankin da ake fama da tashin hankalin book haram.
Yayin da yake yabawa al’ummomin kasashen Turai akan yadda suke rungumar Yan gudun hijirar da suka tsere daga Ukraine, Rocca yace abin takaici baki kadan ne da suka fito daga Afirka ke samun irin wannan tarba bayan tsallake tekun Miditereniya mai dauke da hadari.
Kasashen duniya sama da 150 suka rattaba hannu akan yarjejeniyar magance matsalar karbar bakin dake tserewa daga kasashen da ake fama da tashin hankali a duniya.
A wani labari na daban wani matashin dan bindiga mai shekaru 18 ya bude wuta kan mai uwa da wabi a wata makarantar Firamare da ke Texas na Amurka, inda ya kashe dalibai yara 19 da malamai biyu.
Matashin da ya kai hari makarantar Robb Elementary School mai suna Salvador Ramos ya shiga dakunan karatu daya bayan daya yana harbi, kafin jami’an tsaro su yi nasarar bindige shi har lahira.
Hari mafi muni kan makarantu
Harin makarantar firamare ta Robb da ke garin Uvalde na Latino, shi ne hari mafi muni da ake kai wa makarantun Amurka tun bayan da wani dan bindiga ya kashe yara 20 da manya shida a makarantar Sandy Hook da ke Newtown, Connecticut, a watan Disambar shekarar 2012.
Kuma ya zo ne kwanaki 10 kacal bayan da wani kazamin harin wariyar launin fata da aka kai a wani babban kanti na Buffalo da ke birnin New York, wanda ya kara yawan kashe-kashen jama’a na tsawon shekaru a coci-coci da makarantu da shaguna.
Dokar Mallakar bindiga
Shugaban Amurka Joe Biden wanda yayi Allha wadai da harin, ya sake jadda bukatar garambawul ga dokokin mallakar bindiga, a wani jawabi ga al’ummar kasar sa’o’i bayan harin.