Kotun hukunta manyan laifuffuka da ke birnin Hague (ICC) ta bada umurnin gudanar da bincike akan yakin da kasar Philippines ta kaddamar kan masu mu’amala da miyagun kwayoyi abinda yayi sanadin rasa dimbin rayuka.
Shugaban kasa Rodrigo Duterte ya janye kasar daga cikin kotun a shekarar 2019 bayan ta kaddamar da bincike akan irin wuce gona da iri da hukumomin kasar suka yi wajen yaki da shan kwayoyin.
A shekarar 2016 aka zabi shugaba Duterte bayan da yayi alkawarin kawar da matsalar miyagun kwayoyi a Philippines, in da ya baiwa ‘yan sanda umarnin kashe wadanda ake zargi da tu’ammuli da miyagun kwayoyi.
Akalla mutane dubu 6 da 181 aka kashe tun daga watan Yulin shekarar 2016, kamar yadda kididdigar hukumomin Philippines suka fitar a watan Yulin bana.
Sai dai masu gabatar da kara na kotun ICC, sun kiyasta cewa adadin mutanen da aka kashe ya kai tsakanin dubu 12 zuwa dubu 30 da sunan yaki da ‘yan kwaya.
Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte ya sha alwashin ci gaba da yaki da shan miyagun kwayoyi wanda ya hallaka dubban jama’a a kasar. Duterte wanda ke wannan batu yayin jawabin shekara-shekara kan halin da kasar ke ciki ya ce za su dora kan kokarin da su ke na ganin sun kawar da dabi’ar shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Rahotanni sun ce tun bayan kaddamar da yakin kan sha da safarar miyagun kwayoyi a shekarar 2016 bayan hawa mulkin shugaba Duterte, akalla mutane dubu 4 da 354 aka hallaka bayan kama su da safarar miyagun kwayoyin.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi ikirarin cewa adadin mutanen da aka hallaka sanadiyyar fataucin kwayoyin ya haura linki biyu kan wanda gwamnatin ta Phillippines ta sanar, matakin da suka ce ya zama take hakkin bil’adama.
Jawaban na Shugaba Duterte dai ya zo da tasgaro musamman bayan da wasu taron masu zanga-zanga suka cika titunan kasar tare da neman samar da sauye-sauye a tsare-tsaren gwamnatinsa.