Hungary Ta Takawa (EU) Birki Kan Kakabawa Man Fetur Din Rasha Takunkumi.
Firaministan Hungary, Viktor Orbán, ya takawa kungiyar tarayyar turai birki game da shirinta na kakabawa Rasha man fetur din Rasha takunkumi.
Mista Orbán, ya bayyana shirin a matsayin wani babban cikas ga hadin kan kasashen turan.
Shugaban gwamnatin Hungary, ya bukaci da a janye batun sanya takunkumi kan man fetur din na Rasha da dangoginsa a jerin sabbin takunkuman da EU, ke son sake laftawa Rasha.
Hungary, dai na sayan kashi 65% na man fetur din ta daga Rasha, kuma a cewar shugaban gwamnatin kasar, Budapest, na bukatar akalla shekaru biyar nan gaba kafin ta samu wasu hanyoyi na daina dogaro da man fetur din Rasha.
A ranar Alhamis da ta gabata ce shugabar Kungiyar tarayyar turan, Ursula von der Leyen, ta sanar da shirin EU na kakaba wa Rasha sabbin takunkumai ciki har da haramta sayen man fetur dinta, wanda ta ce Moscow ke amfani da kudaden domin yakar Ukraine.
READ MORE : Abdollahian Da Guteress, Sun Zanta Kan Batutuwa Da Dama Da Suka Shafi Kasa Da Kasa.
Saidai batun kakaba wa Rasha takunkumi kan makamashinta ya haifar da rarrabuwar kai tsakanin kasashen na yamma.
READ MORE : Kungiyoyin Gwagwarmayar Falastinawa Sun Dora Alhakin Abin Da Ke Faruwa A Kan Gwamnatin Isra’ila.