Kasar Hungary ba za ta bai wa kasashen duniya damar kai wa Ukraine makaman da za ta yaki Rasha da su ta sararin samaniyarta ba, bayan da kungiyar kasashen Turai tace zata aikewa kasar makaman yaki.
Ministan ya ce, sun dauki wannan mataki ne domin kare lafiyar jama’ar kasar su dake gida da kuma wadanda ke zama a cikin kasar Ukraine.
Szijjarto ya ce ana iya amfani da safarar makaman wajen kai harin soji wanda ke iya yiwa jama’ar su illa.
Ministan ya ce babban abin da ke gabansu a wannan lokaci shi ne tabbatar da lafiyar kasarsu da kuma jama’arta, saboda haka ba zasu saka hannu a yakin dake gudana a makociyar su ba.
Babban jami’in diflomasiyar kasashen Turai Josep Borrell ya ce zasu bada Euro miliyan 450 domin sayawa Ukraine makaman yakin da za’a mika mata.
A wani labarin na daban Kasar Faransa ta ce yana da matukar muhimmanci a kammala tattaunawar da wakilan kasashen duniya ke yi wajen cimma matsaya kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran a wannan mako.
Kasashen dake cikin yarjejeniyar ta shekarar 2015 na kallon wannan yunkuri a matsayin hanyar da ta rage na hana kasar Iran gina makamin nukiliya zargin da kasar ke ci gaba da musantawa.
Yanzu haka babban jami’in dake wakiltar Iran wajen tattaunawar Ali Bagheri ya koma Vienna daga Tehran inda yaje tuntuba domin ci gaba da shiga taron.
Kasashen dake cikin tattaunawar sun hada da Faransa da Jamus da Birtaniya da Rasha da China da kuma Amurka bayan ita Iran.
Yarjejeniyar ta shekarar 2015 ta ragewa Iran takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakaba mata saboda shirin nukiliyar, amma sai kasar Amurka tayi gaban kan ta wajen janyewa daga cikin ta a shekarar 2018 lokacin jagorancin shugaba Donald Trump wanda ya sake sanyawa Iran sabbin takunkumin karya tattalin arziki.
Wannan mataki na Trump ya sa Iran ta koma ci gaba da shirin tace sinadarin uranium da ake zargin zata gina makamin da shi.
Yayin gudanar da wannan taro na Vienna Iran tayi ta bukatar bata tabbacin cewar gwamnatin Joe Biden ba zata dauki irin matakin da Donald Trump da ya gada ta dauka ba.