Hukumomi a Burkina Faso sun sami nasarar kubutar da yara 374 daga hannun masu safarar mutane zuwa kasashe dake makwaftaka da kasar, dan aikin gona da hakar ma’adanai.
Yaran dai ana fita dasu ne domin aikin gona da sauran ayyukan da suka hada da hakar ma’adinai a wasu kasashe da ke makwaftaka da Burkina Faso.
A cewar Ministan ayyukan jinkai na kasar, Helene Marie Laurence, tuni matakin ya fara shafar al’ummar kasar musamman ma yara tare da kuma martaban kasar a idon duniya.
A bara kawai, yara 2,318 aka kubutar kuma mafi yawancin su ‘yan kasa da shekaru 16.
Akasarin wadannan yaran dai ana kai su kasar Ivory Coast ne kasancewarta kasa mai gonakin Coco da yawa a cewar ma’aikatar Hukumomi na kasar ta burkina faso.
Dubban mutane a Burkina Faso sun gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar inda suke neman gwamnati ta dauki matakan kawo karshen hare-haren ta’addancin da suka addabi sassan kasar.
Karo na farko kenan da ‘yan adawa tare da hadin gwiwar kungiyoyin fararen hula suka jagoranci zanga-zangar matsin lamba ga gwamnatin shugaba Roch Marc Christian Kabore, tun bayan nasarar tazarcen da yayi a zaben shekarar bara.
Tun daga shekarar 2015 al’ummar Burkina Faso suka soma fuskantar hare-haren ta’addancin kungiyoyi masu alaka da Al Qa’eda, tashin hankalin da kawo yanzu ya raba mutane akalla miliyan 1 da dubu 200 da muhallansu, yayin da wasu fiye da dubu 1 da 300 suka mutu.