Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta bayyana irin hukuncin da za ta iya dauka kan Abba Kyari A cewarta, za ta iya korarsa kai tsaye ko rage masa matsayi kamar yadda dokar aikin ta tanada.
A halin yanzu ana ci gaba da bincike kan zargin da ake wa Abba Kyari na karbar cin hanci a hannun Hushpuppi Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta bayyana cewa kora kai tsaye na daya daga cikin hukuncin da ka iya hawa kan mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (DCP), Abba Kyari, idan aka same shi da laifin da ake tuhumarsa da shi.
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta dakatar da Kyari kwanan nan bayan da Amurka ta gabatar da zarginsa da hannu a zambar dala miliyan 1.1 da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushipuppi ya aikata.
A bangaren Kyari, ya karyata dukkan wasu tuhume-tuhumen da ake akansa.
Braimoh ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa hukuncin da ake yiwa jami’an ‘yan sandan da suka aikata irin tuhumar da ake wa Kyari sun hada da gargadi, tsawatarwa, tsawatarwa mai tsanani, rage matsayi, da kora kai tsaye.
Ya ce abin bakin ciki ne cewa masu yaki da aikata miyagun laifuka a wasu lokutan kan tsunduma cikin barna a karshen cikin rashin kulawa. Amma mai magana da yawun PSC ya nuna cewa ba daidai bane a yanke cewa DCP Kyari ya aikata laifi ba tunda har yanzu ba a gurfanar da shi a karkashin dokokin Najeriya ba.
Braimoh ya bayyana cewa tuhumar da ake wa Kyari a kotun Amurka na bukatar a bi dokokin Najeriya da farko don tabbatar da ko dan sandan ya aikata laifi kamar yadda ake zargi.
Ya lura cewa zai zama abin takaici idan aka samu dan sandan da ake yaba aikinsa a kasar. Babban lauya ya ce akwai bukatar mika Abba Kyari ga FBI, ya fadi dalili.
Shahararren lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan adam, Cif Femi Falana (SAN) ya yi kira ga Babban Lauyan Tarayya (AGF) kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya aiwatar da bukatar Amurka ta mika mata Abba Kyari akan ka’ida.
Falana ya ce Kwamitin Bincike na Musamman da Babban Sufeto Janar ya kafa Babban Sufeto kan lamarin da ake dubawa ya kamata ya yi cikakken aiki.
Da yake magana yayin wata hira ta wayar tarho da gidan Talabijin na Afirka mai zaman kansa wanda jaridar Daily Sun ke sa ido, Falana ya bayyana cewa Kyari ya samu ne daga tsarin gwamnatin da ya gaza.
A kalmomin sa yake cewa: “Don kawo karshe da rufe wannan mummunan babi, binciken dole ne ya wuce tuhumar da FBI ta yi, dole ne a bincika lamarin a cikin gida, kuma ba wai a mika Kyari ga Amurka kawai ba.”