Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da yara 13,000 aka kashe a Gaza a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa, inda ta ƙara da cewa yara da dama na fama da rashin abinci mai gina jiki kuma ba su da kuzarin yin kuka.
Dubban mutane sun jikkata ko kuma ba za mu iya tantance inda suke ba. Wataƙila sun maƙale a karkashin ɓaraguzan gine-gine … Ba a taɓa samun yanayin da aka kashe yara da yawa haka ba a duk wani rikici a duniya,” in ji Babbar Daraktar UNICEF. Catherine Russell ta shaida wa shirin “Face the Nation” na CBS News.
“Na kasance a cikin dakunan yara masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki, duk dakin ya yi shiru. Saboda yara da jarirai … ba su da kuzarin yin kuka.”
Russell ya ce akwai “gaggarumin ƙalubale na tsarin mulki” ga manyan motoci masu jigilar kayan abinci zuwa Gaza don ba da agaji.
Netanyahu ya ce ba zai amince da yarjejeniyar zaman lafiya da za ta bar su da ‘rauni’ ba.
Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya ce duk wata yarjejeniyar zaman lafiyar Gaza da za ta raunana Isra’ila tare da hana ta damar kare kanta daga maƙwabta masu gaba da juna, ba za a amince da ita ba.
Duk wata yarjejeniyar zaman lafiya “wadda za ta sa Isra’ila ta yi rauni da kuma kasa kare kanta” ba abin da za ta yi sai mayar da zaman lafiya baya ba a gaba ba,” in ji shi yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz a yammacin Birnin Kudus, yana mai nanata cewa “dole Isra’ila ta samu duk wani tsaro da ya wajaba”.
Netanyahu ya ce Isra’ila ba za ta bar fararen hula da suka maƙale a Rafah ba lokacin da dakarunta suka fara kai farmakin da aka daɗe ana tsammanin kai wa kudancin Gaza inda Falasdinawa sama da miliyan ɗaya suka samu mafaka.
DUBA NAN: Shugaban Kasar Rasha: Putin Ya Lashe Zaben Da Aka Gudanar
“Ba wani abu ne muke yi ba yayin da ake kulle jama’a. Maganar gaskiya ma ita ce za mu yi akasin haka, za mu ba su damar ficewa.”