Hukuma Mai Kula Da Mashigar Ruwa Ta Suiz Ta Ce Ba Ruwanta Da Rikicin Kasar Ukrain.
Hukuma mai kula da mashigar ruwa ta Suez ta kasar Masar ta bayyana cewa ita ‘yar ba ruwanta ne a yakin da ke faruwa a kasar Ukrain, bayan da Amurka ta bukaci kasar Masar ta hana jiragen ruwan Rasha ratsawa ta mashigar.
Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya nakalto Usama Rabi’u shugaban hukumar mashigar ruwa ta Suez yana fadawa tashar talabijin ta “Babban Sauti” ta kasar masar kan cewa mashigar ruwa ta Swuez ta kasa da kasa ce, don haka hukumarsa ba zata shigar da al-amuran siyasa a ayyukanta ba, saboda haka ba ruwanta da daukan bangaren a yakin da ke faruwa a kasar Ukrainn.
Usama ya kara da cewa, sanadiyar karuwan farashin man fetur a duniya mashigar ruwa ta Suez za ta kara kasha 10% na kudaden da jiragen da suke ratsawa ta mashigar zasu biya.
Kafin haka dai shugaban kasar Ukrain ya bukaci kasashen duniya gaba daya su kauracewa kasar Rasha, su hana jiragen samnta sauka a duk duniya, da kuma tashoshin jiragen ruwa gaba daya su hana jiragen ruwan Rasha amfani da su.