Mayakan Houthi sun gargadi kasashe kan su janye jama’arsu daga jiragen ruwan da ke da alaka da Isra’ila.
1325 GMT — Hezbollah da Isra’ila na musayar wuta
An ji karar jiniyar gama-gari a birane da dama na Isra’ila da ke kusa da iyakar Lebanon a ranar Lahadi a daidai lokacin da kungiyar Hezbollah da sojojin Isra’ila ke harba wa juna rokoki.
Rundunar sojin Isra’ila a wata sanarwa ta bayyana cewa ta gano an harba rokoki goma daga Lebanon wadanda ke tafe zuwa garin Shlomi a kusa da iyakar da ke arewa.
Karar irin wannan jiniya akasari alama ce ta harin sama wanda aka kaddamar wa Isra’ila. / Hoto: Getty Images
Sai dai kafar watsa labarai ta Channel 12 ta ruwaito cewa babu wanda ya mutu ko kuma wata asara da aka yi.
1150 GMT — Mayakan Houthi sun sha alwashin kai hari kan duk wani jirgin ruwa na Isra’ila
Mai magana da yawun kungiyar Houthi ta Yemen, Yahya Sarea ya bayyana cewa kungiyar za ta kai hari ga duk wani jirgin ruwa na kamfanonin Isra’ila ko kuma yake dauke da tutar ta Isra’ila, kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta na Telegram.
Yahya Sarea ya bukaci duka kasashen duniya su janye mutanensu da ke aiki a ire-iren jiragen ruwan.
Mayakan na Houthi sun yi wannan barazanar ne a daidai lokacin da adadin mutanen da Isra’ilar ta kashe ya haura 13,300 wadanda akasarinsu yara ne kanana da mata.
0950 GMT — Dakarun Hamas sun ce sun kashe sojojin Isra’ila shida
Dakarun Al-Qassam Brigades na Hamas sun ce sun kashe sojojin Isra’ila shida a unguwar Juhor ad-Dik da ke kudu maso gabashin Gaza.
A wata sanarwa da suka fitar a ranar Lahadi, sun ce sun soma harba musu makamin roka, sai daga baya suka bi su da harbi da bindiga mai sarrafa kanta.
Sojojin na Isra’ila na ci gaba da kutsawa cikin Gaza domin yakar Hamas. / Hoto:Reuters
Zuwa yanzu babu wani karin bayani daga sojojin na Isra’ila kan sanarwar da mayakan na Hamas suka fitar.
0930 GMT — An sake kashe sojin Isra’ila biyu a Gaza
Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa an sake kashe sojojinta guda biyu a Gaza, wanda hakan ya sa adadin sojin Isra’ilar da aka kashe ya kai 59 tun bayan da Isra’ilar ta kaddamar da kai hare-hare ta kasa a cikin Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce akwai karin sojan Isra’ilar daya da ya samu mummunan rauni a yayin da yake yaki a cikin Falasdinu.
Zuwa yanzu sama da mutum 12,300 Isra’ilar ta kashe a Gaza a hare-haren da take ci gaba da kaiwa ba kakkautawa.
0910 GMT — Isra’ila ta kashe mutane da dama a harin da ta kai Khan Younis
Akalla Falasdinawa 15 Isra’ila ta kashe a harin da ta kai Khan Younis da ke kudancin Gaza, da kuma sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, kamar yadda kafar watsa labarai ta Falasdinawa ta ruwaito.
Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan Gaza a kullum inda daruruwan mutane ke mutuwa akasari yara. Hoto/AA
Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ce jiragen yakin Isra’la sun kai harin ne da asubahi a gidaje biyu da ke Khan Younis.
Kamfanin dillancin labaran ya kara da cewa an kashe farar hula 13 a lokacin da jirgin ya kai hari kan gidan iyalan Zuhd da ke sansanin Nuseirat sannan wata mace da danta suka rasu a wani hari da jirgin sojin ya kai a gidan iyalan Abu Akar.
Source: TRTHausa