Sayyid Nasrullah ya bayyana wannan da cewa, kokari ne daga bangaren kasar Iran domin taimaka ma al’ummar kasar Lebanon, sakamakon mawuyacin halin da aka jefa su saboda dalilai na siyasa.
Sannan kuma ya bayyana cewa, a halin yanzu katafaren jirgin ruwan na Iran ya isa gabar ruwa ta Baniyas a kasar Syria, kuma an fara sauke man a can, wanda daga can ne za a shigo da shi yankin Biqa na kasar Lebanon.
Dangane da yadda za a rarraba man kuwa, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, za a raba shi ne a dukkanin yankunan kasar ba tare da la’akari da wani bambanci ba.
Sannan kuma ya jaddada cewa, za a sayar da man ne bayan an karya farashinsa kasa sosai, ta yadda kowa a kasar Lebanon zai iya sayea cikin sauki, kuma tuni Hizbullah da gwamnatin Lebanon sun shiga tattaunawa kan yadda za a kayyade farashin.
Sayyid Nasrullah ya ce babu wani wani zai ci riba da kudi tsakanin Iran da Hizbullah idan aka sayar da wannan mai, domin kuwa farashin da za a sayar da shi bai kai ma kudin man balantana a dora riba akansa, manufar hakan kuma ita ce rage radadin wahala da mutanen Lebanon suke ciki saboda karancin makamshi a kasar.
Baya ga haka kuma ya fatan samun nasara ga sabuwar gwamnati da aka kafa a kasar Lebanon, inda ya kirayi sabon Firayi minista da kuam sauran ministoci gami da ‘yan majalisar dokokin kasar ta Lebanon, kan su sauke nauyin da ya rataya a kansu na yi al’ummarsu aiki, tare da fifita maslahar al’umma da kasa a kan maslaharsu ta kashin kansu.