Hizbullah Ta Sanar Da Sunayen Yan Takararta A Zaben Kasar Mai Zuwa.
Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Sanar Da Sunayen ‘ Yan Takarar Da Ta Tsayar A Zaben Kasar Mai Zuwa
A cikin jawabin da ya gabata a jiya da marece wanda aka watsa ta talabijin, jagoran kungiyar ta Hizbullah, ya ce; A halin yanzu suna cigaba da tuntubar abokansu na siyasa, kuma ana bijiro da ra’ayoyi mabanbanta, domin kulla kawance a yayin zaben.”
Jagoran kungiyar ta hizbullah Sayydi Hassan Nasarallah ya kuma kirayi al’ummar kasar da su kaucewa gaskata labarai marasa tushe da suka shafi harkar zabe da ake watsawa a kafafen sada zumunta.
Sayyid Nasrallah ya kuma kara da cewa; A fili yake cewa a wasu mazabun za mu yi kawance da abokanmu na siyasa domin fito da sunayen ‘yan takara guda tare da su, kuma za su iya banbanta da su a cikin wasu mazabun da hakan zai kasance cikin fahimtar juna.
Sayyid Nasrallah ya kuma ce; Mun riga mun tattauna manufofinmu na yakin neman zabe, kuma nan gaba kadan za mu sanar da su.
Bugu da kari jagoran na kuniyar Hizbullah ya yi ishara da ayyukan da zababbun ‘yan kungiyar ta Hizbullah su ka yi a cikin shekaru hudu da su ka gabata a cikin fagage daban-daban.
A wani sashe na jawabin Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana cewa; Tun tuni ba su saba yi wa mutane alkawulan da ba za su iya cikawa ko lasa musu zuma a baki a yayin yakin neman zabe.