Akalla mutane 23 ne suka mutu a kasar Tanzania bayan hatsarin da ya faru inda wata mota kirar bas tayi taho mu gama da motar dakon kaya a gabashin kasar ranar Juma’a.
Shugaban ‘yan sanda yankin Morogoro dake gabashin kasar, Fortunatus Muslim, ya ce hatsarin ya afku ne a Melela Kibaoni, mai tazarar kilomita 200 daga birnin gabar tekun kuma cibiyar tattalin arziki Dar es Salaam.
“Direban babbar motar da ke kan hanyarsa daga tashar jiragen ruwa ta Dares Salaam zuwa jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, na kokarin kaucewa wani babur ne a lokacin da motocin biyu suka yi karo da juna.
Fadar shugaban kasar da yammacin ranar Juma’a ta ce mutane 22 ne suka mutu yayin da wasu 38 suka jikkata a hatsarin.
A wani labarin na daban daga Tanzaniyan, Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan ta yiwa gwamnatin kwariyar –kwariyar garambawul, sauyin dake zuwa biyo bayan barakar da ake fuskanta a jam’iyyar Chama Cha Mapinduzi dake shugabantar kasar ta Tanzania.
Ranar alhamis da ta gabata dai ne Shugaban majalisar dokokkin kasar ta Tanzania Job Ndugai ya sanar da yin murabis,bayan da ya zargin gwamnatin kasar da ciwo bashi daga kasashen waje ba bisa ka’ida ba.