Gwamnan jihar Tillaberi a jamhuriyyar Nijar Tidjani Ibrahim Katiella ya tabbatar da wani harin kan tawagar motocin shugaban yankin Bankilare da ya hallaka dakarun Soji 6 baya ga jikkata wasu 3 a yankin wanda ke iyakar kasar da Burkina Faso.
Wannan dai ne karon farko da harin mayakan masu ikirarin jihadi ke shafar shugabannin yankin sabanin a baya da sukan farmaki iyakar fararen hula da jami’an tsaro.
Bayanai sun ce dakarun da suka rasa rayukansu a farmakin jami’an tsaro ne na national guard da ke aikin bayar da tsaro ga shugabanni, da manyan ‘yan siyasa a sassan kasar.
Yankin Bankilare da ke da iyaka da kasashe 2 masu fama da hare-haren ta’addanci wato Burkina Faso da Mali shi ne yankin da yafi fuskantar hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi yanzu a jamhuriyyar Nijar.
Ko a litinin din da ta gabata sai da harin mayakan masu ikirarin jihari ya hallaka ‘yan sanda 3 tare da jikkata wasu 7 bayan wani farmaki kansu cikin dare a shingen bincikensu da ke Petelkole.