Harin da Rasha ta kai kusa da kan iyaka sako ne ga NATO – Poland.
Wai harin roka da Rasha ta kai kan wani sansanin sojin Ukraine kusa da kan iyakar kasar da Poland a jiya Lahadi wani kokari ne na razana kungiyart tsaro ta NATO, kmar yada mataimakin ma’aikatar harkokin waje na Poland Marcin Przydacz ya shaida ma BBC.
Akalla mutum 35 ne suka halaka a sanadin harin da aka kai kan sansanin horar da sojoji na Yavoriv wanda ke da nisan kilomita 20 daga kan iyakar Ukraine da Poland, wadda mamba ce ta kungiyar NATO.
Przydacz ya shaida wa BBC cewa: “Lallai suna sane cewa wannan sansanin na kusa da kan iyakarmu da Poland ne.”
READ MORE : Indiya za ta sayi man fetur daga Rasha a farashi mai rahusa.
Ya kuma ce, “Rashawa na son aika wa NATO sako ne a dalilin kai wannan harin… Sna son yi ma NATO gargadi ne.”
Mista Przydacz ya ce yana fargabar abin da ka iya afka ma kasarsa “da ma wasu kasashen tun da Mista Putin na yunkurin lalata wannan duniyar da muke rayuwa cikinta.”
READ MORE : Shin me nene laifukan yaki kuma ko za a iya tuhumar Putin kan Ukraine