Harin Bomb Da Aka kai a Birnin Kabul Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane 5 Tare Da Jikkata Wasu Da Dama.
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Afghanistan ta fuskance tashe tashen bama bamai da hare-haren yan ta’adda a baya bayan nan a wasu yankunnan kasar da suka hada da Kabul Mazar-e-sharif da masallacin Kunduz kuma yayi sanadiyar mutuwa da jikkataan daruruwan mutane masu yawa, kuma dukkansu kungiyar ta’adda ta ISIS ce ke da alhakin kaiwa.
Kungiyar Taliban da ta karbe madafun iko a kasar tun a ranar 15 ga watan Agustan shekara ta 2021 ta I alwashin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin kasar.
Wata majiayr labarai ta tabbatar da kisan wasu mata guda 3 yayin da wasu guda 2 kuma suka jikkata sakamakaon fashewar wani abu a yammacin birnin Kabul a yammacin jiya Asabar, sai dai a kwai yi wuwar adadin wadanda suka mutu ya karu da aka kai su Asibitin wazil Akhbar Khan domin kula da lafiyarsu.
READ MORE : Ma’aikata A Najeriya Sun Gudanar Da Bukin Ranar Ma’aikata Ta Duniya.
Idan anan iya tuanwa a ranar juma’a da ta gabata ma daururwan mutane ne suka yi shahada wasu kuma suka jikkata sakamakon fashewar wani Bomb da aka dana a wani masallacin yan shi’a dake birnin Kabul.