Akalla fararen hula 11 da suka hada da mata hudu da yara kanana uku suka gamu da ajalinsu a kasar Afghanistan, lokacin a wani hari da wata motar bas na safa-safa ta aukawa wani bam da aka dana a gefen hanya, a dai dai lokacin da babban mai shiga tsakani na Amurka Zalmay Khalilzad ke ziyara a Kabul.
Hari na baya-bayan nan da ya rutsa da motocin fasinja ya faru ne a yammacin Asabar a lardin Badghis da ke yammacin kasar, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar sabon rikici a watannin da ke tafe yayin da Amurka ke ci gaba da janye sauran dakarunta da suka rage a kasar.
Babu wata kungiya da ta dauki alhakin fashewar amma gwamnan Badghis Hessamuddin Shams ya zargi Taliban da dana bam din.
Wani jami’in lardin, Khodadad Tayeb, ya tabbatar da adadin kuma ya ce motar bas din ta fada cikin kwari bayan da bam din ya tashi da ita.
Harin na ranar Asabar ya zo ne bayan wasu fashe-fashen da aka auna kan motocin fasinja a Kabul a wannan makon, biyu daga cikinsu a ranar Alhamis a yankunan da galibin ‘yan Shi’ar Hazara suka fi yawa.
Amurka ta sanar da kudurin ta na ficewa daga kasar ta afghanistan amma bayan hakan ba da jimawa sai fashe fashen bama bama suka fara tashi a babban birnin kasar na kabul.
Wancan fashewar ya auku ne a wata makarantar yara kanana mabiya mazhabar shi’a inda kungiyar masu tsatstsauran ra’ayin wahabiyancin na ta taliban ta dauki nayin kaiwa.
Bayan wannan sai kuma wannan hari ya sake aukuwa wanda da dama al’umma suna zargin wani sare sari na kin fitar amurka daga kasar ta Afghanistan.
Mutanen Afghanistan dai sun gaji da zaman sojojin amurka a kasar saboda tabarbarewar tsaro da hari kan fararen hula daya yawaita a kasar mai iyaka da kasar Iran.